Matsalar fashi a teku ta damu Afrika

Taron ECOWAS da CEEAC
Image caption Taron ECOWAS da CEEAC

Shugabannin kasashen kungiyar tattalin Arzikin Afrika ta yamma, ECOWAS da kasashen tsakiyar Afrika, sun fara taron yaki da fashin teku a mashigin tekun Guinea.

A ranar lahadin da ta wuce ne ministocin harkokin wajen kasashen suka gudanar da wani taro na sharar fage, kan babban taron Shugabanninsu, inda suka tsaida manyan batutuwan da taron zai tattauna a kai.

Taron wanda aka bude a birnin Yaonde na Kamaru, ya biyo bayan kudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a bara, wanda ya nemi kasashen Yammaci da Tsakiyar Afrika su dauki kwararan matakai na magance fashin teku a mashigin tekun na Guinea.

Mashigin dai na da albakatun man fetur mafi yawa a duniya, inda yake da gangan danyen mai biliyan 24 wato kusan kashi hudu da rabi cikin dari na ma'adanan man fetur na duniya.

Karin bayani