An yankewa Berlusconi hukunci shekaru 7

Image caption An yankewa Berlusconi hukuncin shekaru bakwai

Wata kotu a Italiya ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai a kan tsohon pirayin ministan kasar, Silvio Berlusconi kan laifin biyan kudi domin yin lalata da wata karamar yarinya dake karuwanci.

Haka nan kuma kotun ta haramta wa Mr Berlusconi sake rike wani mukamin siyasa har karshen rayuwarsa.

Lauyan Mr Berlusconi Niccolo Ghedini ya ce za su daukaka kara.

Ya ce, "mun yi tsammanin hakan, kuma mun dauka ma cewa za a yanke masa wa'adin da ya fi wanda masu gabatar da kara suka nema."

Hukuncin ba zai fara aiki ba sai an saurari daukaka karar.

Mr Berlusconi da yarinyar duk sun musanta yin lalata da juna.

Da ma can an taba yanke ma tsohon pirayim ministan hukuncin dauri kan zamba wajen biyan haraji.

Amma masu aiko da rahotanni na cewa da wuya ne in zai taba kwana a kurkuku, bisa la'akari da sarkakiyar dake tattare da tsarin daukaka kara a Italiya.

Karin bayani