Majalisun Najeriya za su koma bakin aiki

Ginin Majalisar dokokin nijeriya
Image caption Ginin Majalisar dokokin nijeriya

A Najeriya, a yau ne ake sa ran 'yan majalisun dokokin kasar za su koma bakin aiki, bayan wani hutu na makonni biyu.

'Yan majalisar dattawan kasar dai sun tafi hutu ne bayan kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ya gabatar da rahotonsa.

Yayin da 'yan majalisar wakilai suka tafi na su hutun ba tare da cimma matsaya a kan makomar bukatar da shugaban kasar ya gabatar game da yin wasu gyare-gyare ga kasafin kudin kasar na wannan shekarar ba.

Mai yiwuwa dai wannan batu na gyara ga kasafin kudin ya dauki lokaci, saboda 'yan majalisar tun kafin su tafi hutu, sun ce wannan gyara da fadar Shugaban kasar take nema, tamkar wani sabon kasafin kudi ne ta shirya.

Karin bayani