Fashin teku: An bukaci a tura sojin ruwa

Tawagar jiragen yaki
Image caption An samu raguwar fashin take da kashi 78 a gabar tekun Somalia a shekarar 2012

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma sun bukaci a tura dakarun sojin ruwa na kasa da kasa gabar tekun Guinea, domin magance matsalar fashin teku.

Matsalar na bukatar makaki "kwakkwara" Inji shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara a yayin taron kungiyar.

Masu aiko da rahotannin sun ce, gabar tekun Najeriya nan ne inda aka fi samun fashin teku a yankin na yammacin Afrika.

A lokacin da yake jawabi a taron shugabannin yammaci da tsakiyar Afrika a Yaounde, Ouattara yace "Ina kira ga kasashen waje da su taimaka a gabar tekun Guinea da irin kwararan matakan da suka dauka a gabar tekun Aden."

Shi ma shugaban Kamaru, Paul Biya yace akwai bukatar a dauki mataki game da matsalar domin kare hanyoyin jiragen ruwa da kuma tattalin arzikin yankin.

A halin yanzu dai ana samun 'yan fashin teku a gabar tekun yammacin Afrika fiye da na Somalia, a cewar hukumar sa ido kan sufurin jiragen ruwa na kasa da kasa.

Sintirin da jiragen yaki ke yi a gabar tekun Somalia ya rage yawan fashin teku a can.