Obama da Karzai za su tattauna da Taliban

Dan kungiyar Taliban
Image caption Dan kungiyar Taliban

Amurka ta ce ita da Afghanistan, a shirye suke su tattauna tare da kungiyar Taliban, bayan wani hari da 'yan bindigar suka kai kan fadar Shugaban Kasar dake Kabul a ranar litinin.

Fadar gwamnatin Amurka watau White House ta ce Shugaba Barak Obama da takwaransa Hamid Karzai, sun yi magana ta bidiyo, bayan harin da aka kai kan cibiyar hukumar leken asiri ta CIA, da kuma gine ginen gwamnati.

Shugabannin biyu dai sun sake nanata cewa Afghanistan din ce za ta jagoranci sasantawar, inda wakilan gwamnatin kasar za su tattauna kai tsaye da 'yan kungiyar ta Taliban.

Karin bayani