Ma'aikata nawa Afirka za ta iya samarwa a duniya?

Alummar Afrika ta Kudu
Image caption Alummar Afrika ta Kudu

Ko kashi 40 na ma'aikata a duniya za su kasance 'yan Afirka nan da 2050? Binciken da aka gudanar na wannan ikirari da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi, ya fito da wasu bayanai masu ban mamaki game da sauyin da ake samu a yawan al'ummar duniya nan gaba.

''Abin da na gani a Afirka, abin da na gani a duniya, shi ne karuwar yawan matasa, kuma nan da shekaru 35 Africa za ta samar da kashi 40 cikin dari na ma'aikata a duniya.''

Ta yiwu wasu daga cikin mutanen da John Kerry ya yi wannan jawabin a gabansu a Jami'ar Addis Ababa da ke Habasha sun cika da mamaki a watan da ya gabata, yayinda yake amasa tambayoyi a wani shirin Hardtalk na BBC da aka nada.

Shin gaskiya ne kuwa batun da ya yi na cewa kashi 40 cikin dari na ma'aikata a duniya za su fito ne daga Afirka nan da shekaru masu zuwa?

Bayanin da Sashen Kidaya na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a baya-bayan nan ya yi bayani daban da na Mista Kerry.

Yawan 'yan Afirka 'yan shekara 25 zuwa shekara 59 wadanda aka kasafta a matsayin shekarun aiki, ana sa ran za su kai biliyan daya nan da shekarar 2050.

A cewar babban jami'in kididdiga na Majalisar Francois Pelletier, hakan na nufin yawan ma'aikatan da Afrika za ta samar a duniya zai karu daga kashi goma sha biyu cikin dari zuwa kashi ashirin da uku cikin dari.

Ke nan, nan da shekaru 35 ko fiye da haka, yawan ma'aikata a duniya wadanda ke zaune a Afirka zai ninka, kuma za su kai kusan kashi daya cikin hudu na ma'aikatan duniya.

Wannan adadi yana da yawa, amma bai kai wanda John Kerry ya fada ba na kashi 40 cikin dari.

Daga ina ya samu wannan alkaluma?

Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Da alama ya yi kuskure ne a maganar da ya yi, kamar yadda ya yi a jawabinsa na farko a matsayin sakataren harkokin wajen Amurka, inda Kerry ya kirkiro da wata sabuwar kasa mai suna ''Kyrzakhastan''.

Ta kuma bayyana cewa kwana daya kafin ya yi wa Jama'a jawabi a jami'ar Addis Ababa, ya gabatar da wani jawabin a wajen taron cika shekaru 50 na kungiyar Tarayyar Afirka, inda ya kusan yin daidai wajen bayyana adadin yawan ma'aikatan da za a samu nan gaba a Afirka.

A lokacin jawabin, Kerry ya yi amfani da kashi 40 cikin dari wajen bayyana wani batun.

Ya ce nan da shekaru masu zuwa, fiye da kashi 40 cikin dari na dukkan matasan duniya za su kasance ne a Afirka.

Hakan zai iya zama gaskiya kuwa?

A yanzu haka kashi 18 cikin dari na matasan duniya sun fito ne daga Afirka kamar yadda kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta ce. Amma adadin ka iya kai wa kashi 33 cikin dari nan da shekarar 2050, sannan kashi 45 cikin dari a shekarar 2100.

Anan ana iya cewa John Kerry ya kusa yin gaskiya.

Ana sa ran Najeriya za ta kasance a gaba-gaba a cikin kasashen da za su samu bunkasar al'umma a nahiyar Afirka.

Kamar yadda Sarah Walters ta makarantar nazarin lafiyar al'umma da cututtukan yankuna masu zafi da ke London ta ce ''Nan da shekarar 2050, Nijeriya za ta kasance a sahun gaba na kasashen da al'umar su ke karuwa a duniya, za kuma ta kasance tana samar da kashi daya cikin biyar na bunkasar al'umma a duniya kafin wannan lokacin''.

A yanzu haka dai Najeriya na da kashi 13 cikin dari na yawan al'umma a nahiyar Afirka, amma ana sa ran adadin zai iya karuwa zuwa kashi 17.5 cikin dari nan da shekarar 2050 sannan kashi 22 cikin dari nan da shekarar 2100. Yawan al'umarta zai karu a wannan lokacin daga miliyan 174 zuwa miliyan 440 a tsakiyar karni, da kuma miliyan 914 a karshen karnin 1, a wanna lokacin za ta kusan riskar China a yawan al'umma.

Sarah Walters ta kuma kara da cewa, ana sa ran samun bunkasar al'umma a nahiyar Afrika fiye da sauran nahiyoyi ne saboda yawan haihuwa da ake yi a yankin.

Image caption Taswirar haasshen yawan al'umar duniya