'Equador ta gaji da barazanar Amurka'

Kasar Equador ta ce za ta janye daga wani shirin bayar da garabasar cinikayya tsakaninta da Amurka, bayan da wasu 'yan siyasar Amurkar suka ce shirin cinikayyar zai sami nakasu idan Equador ta baiwa tsohon jami'in leken asirin da Amurka ke nema ruwa a jallo, Edward Snowden, mafakar siyasa.

Shi dai Mr Snowden ya tona asirin yadda Amurkar ke leken asirin jama'a ta hanyar intanet da wayoyin da suke bugawa, duka a cikin kasar da kuma waje.

Ministan sadarwa na kasar Ecuador, Fernando Alvarado, ya ce yarjajeniyar kasuwancin mai garabasa da suka kulla da Amurka ta zama wani makami da Amurkan ke amfani da shi wajen yiwa kasarsa barazana, don haka Ecuador din ta yi watsi da wannan yarjajeniyar, in don ita a kai kasuwa.

Hakan na faruwa ne kwana daya bayan da shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar Dattawan Amurka, Bob Menendez, ya gargadi Ecuador da cewar yarjajeniyar za ta shiga tsaka mai wuya, idan har ta bada mafakar siyasa ga Mr Snowden.

Ganin yadda dangantaka ta yi tsami a 'yan shekarun nan tsakanin kasashen biyu, musamman bayan da Ecuador ta bada mafakar siyasa ga mutumen nan da ya kafa sashen internet na Wikileaks mai fasa kwai, Julian Assange, da ma zai yi wuya 'yan majalisar dokokin Amurka su goyi bayan a sabunta yarjajeniyar kasuwancin mai garabasa.

Karin bayani