Obama zai gana da Mackey Sall a Senegal

Barack obama a lokacin da ya isa Senegal
Image caption Ana sa ran Mr. Obama zai yaba da zaman lafiya a Senegal

Shugaban Amurka Barack Obama zai gana da shugaban Senegal, Mackey Sall a ziyarar mako da ya fara a nahiyar Afrika.

Baya ga Senegal dai Shugaban zai ziyarci Afrika ta Kudu da Tanzania a ziyararsa karo na biyu a nahiyar ta Afrika.

Jami'an Amurka sun ce Mr. Obama na rangadin kasashen uku ne, da nufin karfafa samun shugabanci nagari da bunkasa tsarin dumokradiyya.

Sai dai ana ganin rashin lafiyar tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela zai dauke hankali, a ziyarar da Obaman zai kai Afrika ta Kudun.

Fadar gwamnatin Amurkan ta ce za ta bar batun duba Mandela ga iyalan tsohon shugaban, ko Madiva zai iya karbar Mr. Obama a halin da yake ciki ko kuma a'a.