Dokar ba da damar amfani da kwayoyin halitta a Birtaniya

jariri

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta samar da daftarin doka nan gaba a cikin shekarannan domin ba da damar amfani da kwayoyin halittar wasu mutane uku domin tagwaita jariri.

Hakan zai sa Birtaniya ta zama kasa ta farko da ta ba da damar yin hakan, abin da masana kimiyya ke dauka da halitta mutum.

Manufar yin hakan dai ita ce baiwa mace da namijin da suke tare wadanda ke fuskantar matsalar yada wata nakasta ko illar jiki ga 'ya'yan da za su haifa damar amfani da kwayoyin halitta masu lafiya.

Wakilin BBC na fannin harkokin kula da lafiya ya ce ba da damar amfani da wannan fasaha zai zama gagarumar nasara ga kimiyya da al'ada da kuma al'umma, saboda hakan zai kawar da damar yada kwayar halittar da ke da illa ga zuriyar da za a haifa a gaba