Shirin inganta tsaro a Yammacin Afrika

ecowas
Image caption Laftanan janarar Sumaila Bakayoko

Manyan hafsoshin sojan kasashen kungiyar ECOWAS ko Cedeao ta yammacin Afrika sun kammala taron yini biyu inda suka tattauna a kan al'amarin Mali da sauran sha'anin tsaro a yankin na yammacin Africa.

A jawabinsa na rufe taron da aka yi a Accra babban birnin kasar Ghana, Shugaban kungiyar manyan hafsoshin sojan Laftanar Janar Sumaila Bakayoko ya ce a shirye suke su tunkari duk wata barazanar tsaro da yankin yammacin Afrika zai fuskanta.

Ya kuma ce zasu dau mataki kan masu kamun kifi ba tare da izini ba a tekun Atlantika abun da ya ce ke janyowa yankin asarar biliyoyin daloli.

Laftanar Bakayoko ya ce kasashen yankin zasu yi aiki tare domin magance matsalar