Rikicin gwamanoni ya dau wani sabon salo

governors
Image caption Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso daya daga cikin gwamnonin jihohin Najeriya

Rikicin shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya ya kai ga sanadin saba wasu al'adu da aka saba yi a sha'anin mulkin kasar, musamman a lokacin da ake gudanar da taron majalisar koli ta tattalin arzikin kasar a jiya Alhamis.

Shugabancin ya dare ne gida biyu, da na Gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameichi da na takwaransa na jihar Plateau Jonah Jang.

Wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman gwamnoni a zauren taron sun tilasta wa gwamnonin biyu, wadanda kowanne ke ikirarin cewa shi ne shugaban kungiyar zama kafada-da-kafada da juna.

Wakilin BBC ya ce rarrabuwar kawuna dake tsakanin gwamnoni ta sa wasu'yan kasar fargabar cewa da wuya a ga alheri a zubukan da za a yi nan gaba.

A cewarsu idan gwamnoni 36 basu iya gudanar da karbabben zabe tsakaninsu ba , da wuya na kasa a dace.