Kudurin kawo sauyi a tsarin shige da fice na Amurka

'Yan majalisar dattawa a Amurka
Image caption Wasu 'yan Majalisar dattawa a Amurka

Majalisar dattawan Amurka ta amince da wani gagarumin kudurin doka mai takaddama da zai kawo sauyi a tsarin shige da fice na kasar.

Kudurin wanda Shugaba Obama ke marawa baya , ya ba da dama ta shekaru 13 da za ta kai ga samun ikon zama dan kasa ga bakin haure sama da miliyan 11 a Amurka.

Hakazalika kudurin dokar ya amince a inganta tsaro a iyakar dake tsakanin Amurka da Mexico, inda za'a samar da karin sabbin jami'an shige da fice dubu ashirn da naurorin sanya ido na zamani

Sai dai kudurin na bukatar amincewar Majalisar wakilai inda yan jamiyyar adawa ta Republicans ke da rinjaye, Kuma wanan babban kalubale ne saboda da dama daga cikin yan jamiyyar Republicans na dari- dari kan batun yin afuwa ga wadanda suka karya doka