Tattaunawa da 'yan kungiyar Taliban

kungiyar Taliban
Image caption Offishin kungiyar Taliban a birnin Doha

Babban kwamandan sojojin Burtaniya a Afghanistan ya ce tun shekaru goma da suka gabata lokacin da aka hambarar da Taliban daga mulki ya kamata a ce kasashen yamma sun tattauna da kungiyar.

Janar Nick Carter ya ce a wannan lokaci ne ya fi sauki a dauki matakin siyasa kan rikicin na Afghanistan lokacin da aka tarwatsa 'yan kungiyar.

Kokarin tattaunawa da 'yan kungiyar ta Taliban a Doha a makon da ya gabata ya ci tura.

Da yake hira da jaridar Guardian ta Burtaniya Janar Carter, ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin Afghanistan ba za ta iya iko da kasar baki daya ba a shekaru masu zuwa, saboda karfin da Taliban ke da shi.

A shekara ta 2014 ne sojojin kasashen yammacin duniya za su bar kasar ta Afghanistan.