Masu zanga-zanga na dafifi zuwa dandalin Tahrir

Masar zanga_zanga
Image caption Masu zanga-zanga a Masar

Dubban 'yan kasar Masar na dafifi zuwa dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira , a shirin gagarumar zanga zangar da za a yi yau Lahadi da nufin tilastawa shugaban kasar Mohammed Morsi ya sauka daga mulki.

Masu adawa da shi sun zarge shi da gazawa wajen magance matsalolin tattalin arziki da na tsaron kasar kuma a cewarsu mutane sama da miliyan 22 ne suka sanya hannu a takardar bukatar neman a gudanar da wani sabon zabe na gaggawa a kasar.

Sai dai suma magoya bayan shugaban wanda ya zama shugaba na farko da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya cikin walwala shekara daya da ta gabata , suna dafifin nasu gangamin.

Sojojin kasar ta Masar sun yi gargadin cewa zasu dauki mataki idan zanga zangar da ake saran yi a fadin kasar ta kazanta.