Kasashen Turai sun nuna bacin rai

Edward Snowden
Image caption Edward Snowden tsohon ma'aikacin leken asirin Amurka

'Yan siyasar kasashen Turai sun nuna bacin ransu game da rahotannin da suka ji cewa ,Amurka ta yi amfani da na'urorin satar daukar bayanai a ofisoshin kungiyar kasashen Turai ta EU da ke Washington, kuma ta yi satar shiga na'urorin kwamfutar ofisoshin.

Shugaban Majalisar Dokokin kungiyar kasashen Turan ya ce idan ta tabbata cewa wannan zargin da wata mujallar kasar Jamus Der Spiegel ta bayyana haka yake to kuwa ba shakka zai zama wata babbar matsala a dangantakar kungiyar kasashen Turai da Amurka.

Ministan harkokin waje na Luxembourg , ya ce rahoton ya bata masa rai matuka, ya bayyana aikin sanya ido na Amurka da cewa abin ya wuce kima kuma.

Mujallar ta Jamus ta ce bijirarran tsohon ma'aikacin leken asirin nan na Amurka , Edward Snowden, shi ne ya nuna mata takardun sirrin da ke dauke da wannan bayani.