Kotu ta soke nadin shugabannin sojin Najeriya

Wata Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta yi shelar cewa nadin da aka yiwa dukkanin manyan hafsoshin rundunonin sojan kasar ya sabawa tsarin mulkin kasar.

Kotun, wadda ke zama a Abuja, karkashin jagorancin Mai Shari'a Adamu Bello, tace nadin shugabannin rundunonin kasar ya haramta, don haka ta soke shi.

Haka nan kuma kotun ta gargadi shugaban kasar da kada ya nada wasu akan wadannan mukamai ba tare da amincewar Majalissar Dattawan kasar ba.

Wadanda wannan shari'a ta shafa dai su ne shugabannin rundunonin mayakan ruwa da na kasa da na sama.

Wani lauya mai zaman kansa ne, Mr Festus Keyamu, ya shigar da karar tun shekara ta 2008.

Ya gaya wa BBC cewa ya gamsu da hukuncin da kotun ta yanke.

Kakakin Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriyar, Dr Reuben Abati, ya ce gwamnati za ta yi nazarin hukunci kafin ta maida martani akan sa.