Rundunar sojan Masar ta gargadi 'yan siyasa

Shedikwatar 'yan uwa Musulmi ta Masar
Image caption An kashe mutum 8 a Masar

Rundunar sojan Masar ta ba 'yan siyasa na dukkan bangarori kwanaki biyu na su warware takaddamar siyasar da aka shiga yanzu, in ba haka ba ta dauki matakin abin da take ganin zai fi zamewa kasar alheri nan gaba.

A wani jawabi da aka watsa ta talibijin, babban hafsan dakarun kasa na kasar ta Masar, Janar AbdulFattah al-Sisi, ya bukaci yan siyasar da su amsa abin da ya kira ,kiran jama'a.

An kashe mutane takwas a wajan hedikwatar jam'iyyar Masar mai mulki, an kuma ruwaito cewa ministoci guda hudu sun yin tayin sauka daga kan mukamin su.

Kwana guda bayan da miliyoyin 'yan Masar suka fantsama kan tituna suna bukatar Shugaba Morsi ya sauka, masu zanga zanga sun farma shedikwatar 'yan uwa musulimin a birnin Alkahira.

Ministocin da suka yi tayin barin mukamansu sun hada da na yawan bude ido da kuma na muhalli.

Kungiyar da ta shirya zanga zangar ranar lahadi ta Tamarod, ta baiwa Shugaba Morsi har zuwa yammacin ranar Talata da ya sauka.

Karin bayani