Cutar Kwalara a Jumhuriyar Nijar

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar Asusun kula da kananan yara na MDD, UNICEF ya ce mutane 331 ne suka kamu da cutar kwalara a Jahar Tillabery da ke yammacin kasar, yayinda goma daga cikinsu suka rasa rayukansu daga farkon shekara zuwa yanzu.

Hukumomin kiwon lafiya dai sun tabbatar da haka ko da yake sun ce lamarin ya yi sauki, a sakamakon ayyukan rigakafi da daukar dawainiyar marassa lafiyan da gwamnatin ke yi, tare da abokan arziki irinsu UNICEF da UNHCR da sauransu.

Amma kungiyar ta UNICEF ta ce akwai bukatar ci gaba da samar da magunguna da wayar da kan jama'a game da matakan tsabta, ganin cewa shan gurbataccen ruwa ne ke haddasa cutar.

Karin bayani