Obama na ziyara a Tanzania

Shugaba Obama a Tanzania
Image caption Shugaba Obama a Tanzania

Shugaba Obama ya isa Tanzania, a matakin karshe na rangadin da yake a nahiyar Afirka, kuma ya sami kyakyawan marhabun.

Tawagar Shugaba Obaman ta hada da daruruwan hamshakan 'yan kasuwa.

Ana sa ran cewa, batun cinikayya zai kasance a saman ajandar tattaunawar da zai yi da mai masaukinsa, shugaba Jakaya Kikwete.

Mista Obaman zai kuma ziyarci wata tashar samar da wutar lantarki, mallakar Amurka.

An rufe hanyoyin mota, an kuma tsaurara matakan tsaro a Darus Salam, babban birnin kasar.

A karshen makon nan ne ya bayyana wani shiri na biliyoyin daloli, na kara samar da wutar lantarki a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara.

Karin bayani