An rufe layukan waya marasa rajista a Najeriya

Image caption Ofishin hukumar sadarwa ta Najeriya

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ta ce ranar Litinin za ta rufe layukan wayoyin salula na mutanen da ba su yi rijistar layukansu ba a fadin kasar.

Ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni ne dai wa'adin da hukumar ta diba wa mutanen dake da wayoyin salula da su yi rajistar ya kare.

Daraktan hulda da jama'a na hukumar, Mr. Tony Ajebor, ya shaidawa BBC cewa sun kwashe shekaru biyu suna rokon jama'a su yi rijistar layukan wayoyin nasu, amma mutane da yawa ba su yi ba domin haka za a rufe layukan wayoyinsu.

A cewarsa, mutane da dama sun yi zaton yin rijistar ba shi da muhimmanci shi yasa ba su yi ba.

Mr. Tony Ajebor ya bayyana cewa sun dauki matakin yi wa layukan wayoyin rijista ne, saboda tabbatar da tsaro a kasar.

Wayar ta salula dai ta soma yawaita a Najeriya ne kimanin shekaru goma sha biyu da suka gabata, inda wasu alkaluma na hukumar sadarwa ke cewa, fiye da mutane miliyan dari ne ke amfani da wayoyin salula a kasar.

Karin bayani