Morsi na kara shiga tsaka mai wuya

Dubun-dubatar Misrawa da ke neman lallai sai shugaban Masar, Mohammed Morsi, ya yi murabus, sun sake cika Dandalin Tahrir da tituna da ke zuwa fadar shugaban kasa a birnin Alkahira.

Suna wasan wuta don murnar abin da suke gani a matsayin gabatowar karshen mulkin Shugaba Morsi.

Sai dai ita ma jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi ta Shugaba Morsin, ta fito da karfinta, inda take kira ga magoya bayanta da su shiga cikin zanga-zangar kare mulkinsa.

An ba da rahoton kafsawa tsakanin bangarorin biyu.

Gobe Laraba da yamma ne wa'adin da soji suka bayar yake cika, wanda ke cewa lallai sassan biyu su cimma sasantawa.

Wasu majiyoyi na soji a Masar sun bai wa BBC bayanin abin da sojin Masar din suka bayyana da taswirar makomar kasar.

Shirin ya hada da dakatar da sabon tsarin mulkin da aka yi mujadala a kai, wanda masu adawa da Shugaba Morsi ke cewa an gaggauta zartar da shi don a tabbatar ya yi daidai da tsarin masu kishin Islama.

Shirin ya kuma ce za a rusa majalisar dokokin da masu kishin Islamar suka fi yawa a ciki, tare da yin sabon zabe.

Babu tabbas a kan kowace irin rawa Shugaba Morsi zai taka - in har akwai - a shirye-shiryen da za su kai ga yin sabon zaben shugaban kasa.

Karin bayani