'An ci zarafin fararen hula a Najeriya'

Sojojin Najeriya
Image caption Hukumar ta ce jami'an tsaro sun kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba

Hukumar kare hakkin bil adama ta Najeriya ta ce tana da kwararan hujjoji da ke nuna cewa jami'an tsaro sun ci zarafin mutane tare da yi musu fyade.

Haka kuma hukumar ta ce jami'an na gallaza wa fararen hula da daure su ba bisa ka'ida ba a kokarinsu na fatattakar 'yan tawaye da ke arewa maso yammacin kasar.

A wani kwarya-kwaryan rahoton da ta fitar, hukumar ta ce tashe-tashen hankula sun sanya dubban manoma barin gonakinsu, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayan abinci.

Hukumar ta ambato rahoton 'yan sanda a kan abin da ya faru a kauyen Baga, inda jami'an tsaro suka bude wuta a kan mutanen da ba-su ji ba-ba-su-gani-ba a lokacin da aka kashe wani soja.

Rundunar sojin dai ta sha musanta cewa tana amfani da karfin da ya wuce kima a kokarinta na dakile hare-haren da masu tayar da kayar baya ke kai wa.

Karin bayani