Snowden ya zargi Amurka

Image caption Snowden ya ce yana da 'yancin bai wa jama'a bayanan da suka shafi rayuwarsu

Tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin Amurka CIA, Edward Snowden, ya zargi Amurka da kaddamar da farautarsa ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma matsawa wadansu kasashe lamba domin ganin sun hana shi mafakar siyasa.

A kalamansa na farko a bainar jama'a tun bayan isarsa filin jiragen sama na Moscow fiye da mako guda, Edward Snowden ya ce har yanzu fa yana da 'yancin bayar da bayanan da suka shafi jama'a.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Mista Snowden ba dan leken asirin Rasha ba ne.

A cewarsa, ''Mista Snowden ba dan leken asirinmu ba ne, kuma bai taba zama dan leken asirinmu ba, kuma ba zai zama ba yanzu. Haka kuma ma'aikatan leken asirinmu ba su taba yin aiki da shi ba, kuma ba za su yi ba''.

Tun da fari wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Rasha, ya ce Mista Snowden ya gabatar da bukatar neman mafakar siyasa ga kasar.

Karin bayani