'Sojoji sun kashe 'yan bindiga sama da dari a Plateau'

Janar Ihejerika, babban hafsan dakarun kasa na Nijeriya
Image caption Janar Ihejerika, babban hafsan dakarun kasa na Nijeriya

Rundunar sojan Najeriya ta ce, dakarunta sun kashe 'yan bindiga fiye da dari, wadanda suka yi amunnar cewa, sune suka kai hare-hare a makon jiya, a wasu kauyuka uku na jahar Plateau.

Manjo Janar Henry Ayoola ya ce, rundunarsa ta musamman ta yi nasarar tabbatar da tsaro a Plateau ta tsakiya, inda akalla mutane ashirin da takwas suka hallaka a tashin hankalin.

Haka ma, an kona gidaje masu yawa a lokacin hare-haren, wadanda aka dangantaka da lamarin satar shanu.

Jihar Plateau dai ta dade tana fama da tashin hankali mai nasaba da kabilanci da kuma addini, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da kuma barnata dukiya mai dimbin yawa.