An tono gawarwakin 'ya'yan Mandela

Babban jikan Mandela, Mandla Mandela
Image caption Babban jikan Mandela, Mandla Mandela

'Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce an tono gawarwaki uku daga garin da jikan Nelson mandela, Mandla yake, a kokarin aiki da umurnin kotu game da wata jayayya da ta kaure tsakanin iyalan game da binne wasu gawarwaki.

Wata kotu a Afirka ta kudu ce ta bada umarnin sake tono gawawwakin 'ya'yan Nelson Mandela tare da sake binne su a makabartar iyalan Mandelan.

Alkalin kotun dake Mthatha na lardin Gabashin Cape ne ya umarci jikan Mandela wato Mandla da ya zartar da umarnin kotun ba tare da bata lokaci ba.

Kotun dai ta yi watsi da da'awar Jikan Mandelan wanda ya tono gawawwakin shekaru biyu da suka wuce ya sake musu matsuguni ba tare da amincewar sauran iyalan ba.

Mandla Mandela, wanda shi ne babban namijin da zai yi gadon mista Mandela, ya tono gawarwarkin ne daga inda aka binne su, a kauyen Qunu, ya kaisu ya binne a kauyen Mvezo da ke kusa da wurin.

Ana zargin yayi hakan ne ba da son ran sauran iyalan Mandelan ba.

A yanzu lauyoyinsa sun shigar da wata sabuwar kara.

Hakan na faruwa ne yayin da tsohon shugaba Nelson Mandela yana can kwance a asibiti, rai kwakwai-mutu-kwakwai.