Yahoo ya sayi manhajar Qwiki

Kamfanin Yahoo
Image caption Alamun kamfanin Yahoo

Yahoo ya sayi Qwiki, wata manhajar da ake amfani da ita a wayar komai da ruwanka ta iPhone.

Manhajar na baiwa mai amfani da wayar damar juya hotuna da waka da bidiyo nan take zuwa fim din da ba shi da tsawo.

Yahoo ya shiga sayayya, a yayin da yake neman sake janyo masu tallata kaya da masu ziyartar shafin daga abokan hamayyarsa, kamfanin matambayi ba ya bata na Google da kuma shafin sada zumunta na Facebook.

A baya-bayan nan Yahoo ya sayi shafin Tumblr na rubuce-rubucen kasidu a intanet da kuma Bignoggins wanda ya shahara wajen yin manhajar wasanni ga wayar komai da ruwanka.

Yahoo bai bayyana ko a kan nawa ya sayi Qwiki ba.

Sai dai masu rubutun kasidu a shafin intanet na 'AllThingsD' ya rawaito cewa an cimma yarjejeniyar ne a kan kudi dalar Amurka miliyan 40 zuwa 50.

Wata sanarwa da Yahoo ya fitar ta ce zai ci gaba "da taimakawa manhajar ta Qwiki kuma ma'aikatansa za su koma ofishin Yahoo dake birnin New York, domin sake fasalin kwarewar Yahoo na ba da labarai".

Farfado da Yahoo

Yahoo na cikin shafukan farko a intanet kuma ya samu nasarori da dama a yayin da kasuwar intanet ke kara bunkasa.

Sai dai a 'yan shekarun baya-bayan nan ya yi ta fadi-tashi a lokacin da gasa ta karu, bayan fitowar kamfanin Google da kuma fitowar dandalolin sada zumunta daban-daban, kamarsu katafaren dandalin nan na Facebook.

A wani yunkuri na sake farfadowa, a bara Yahoo ya baiwa tsohuwar shugabar Google, Marissa Mayer, matsayin wacce za ta jagoranci kamfanin.

Image caption Sabuwar shugabar kamfanin Yahoo, Marissa Mayer

A watan Yulin shekarar 2012 ne Marissa ta kama aiki, inda ta fara saye wadansu kamfanoni a shirinta na sake farfado da Yahoo.

Kuma tun zuwanta ta sayi kamfanoni da dama kamar su Alike da Stamped da Snip.it da kuma Summly, wata manhaja da wani saurayi a Birtaniya ya kirkiro.

A watan Mayu, Yahoo ya sake fasalin tsarin rarraba hotunansa na Flickr, inda ya baiwa masu amfani da shi damar adana har na 1TB ba tare da ko sisi ba.

Haka kuma masu amfani da tsarin za su iya adana bidiyo da manyan hotuna.