Tarihin Adly Mahmud Mansour

Adly Mahmud Mansour
Image caption Sabon shugaban rikon kwaryan Masar ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Alhamis

Shugaban kotun kolin tsarin mulki na Masar, Adly Mahmud Mansour ya zamo shugaban rikon kwarya, bayan tumbuke Shugaba Mohammed Morsi.

Dakarun sojin kasar ta Masar sun jingine tsarin mulki a ranar 3 ga watan Yuli, kuma hafsan sojin kasar janar Abd-al-Fattah Al-Sisi ya sanar da cewa Mr. Mansour zai karbi jagorancin kasar kafin a yi sabon zabe.

Mr. Mansour ya kasance mataimakin shugaban kotun tsarin mulkin tun shekarar 1992, kuma an ba shi matsayin shugaban kotun a shekarar 2013, inda ya kama aiki a ranar daya ga watan Yuli.

Wani shafin intanet na Masar, Masrawi ya bayyana Mr. Mansour a matsayin mutum ne "Miskili" dake kauce wa kafafen yada labarai.

An haife shi a Alkahira a shekarar 1945 kuma ya samu lasisin aikin lauya a shekarar 1967 daga jami'ar Alkahira.

Yayin da ya shiga majalisar kasa a shekarar 1970, inda ya rike mukamai da dama, har zuwa lokacin da ya zama mataimakin shugaban kotun tsarin mulki na kasar a shekarar 1992.

Shi ne ya jagoranci bahasi a kan tsarin mulkin da aka yi a shekarar 2012, wanda ya soke dokar data hana wadanda suka rike mukamai a gwamnatocin baya shiga zabe.

Kuma dokar ce ta baiwa tsohon firai ministan zamanin Hosni Mubarak, wato Ahmad Shafiq damar shiga takarar shugabancin kasar a zaben da aka yi.

Fitowarsa

An fara ganin sunan Mr. Mansour a matsayin wanda zai jagoranci Masar a ranar 30 ga watan Yuni.

A ranar farko na zanga-zangar wato 30 ga watan Yuni ne, wata kungiya mai suna "Al-Sha'ab Yureed (Bukatar Al'umma) ta rarraba wata wasika a tsakanin masu boren, tana mai kira da a nada majalisar da za ta shugabanci kasar, ta kuma sanya sunansa a matsayin wanda yakamata ya zamo mamba.

Shafin intanet na Masrawi ya bayyana wannan lokacin da cewa "An samu sauyi cikin gaggawa" ga Mr. Mansour, wanda ya shafe shekaru goma yana rike da mukami na biyu a kotun tsarin mulkin.

Kuma tun kafin ya fito bainar jama'a ya yi jawabi, da alamu masu ziyarar shafin Twitter sun karbi yiwuwar kasancewar Mr. Mansour a matsayin shugaban rikon kwarya.

A yayin da yake magana da Al-Ahram Al-shabab, Alkali Hamid al-Jamal ya bayyana Mr. Mansour da cewa mutum ne mai shiru-shuru dake da nutsuwa wanda ke yin adalci wajen yanke shawara, kuma wanda zai mutunta bukatun Misirawa.