Adly Mansour ya gayyaci Yan Uwa Musulmi

Adly Mansour, Shugaban rikon Masar
Image caption Adly Mansour, Shugaban rikon Masar

Kwana guda bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Muhammad Morsi, shugaban kasar Masar na rikon kwarya, Adly Mansour, ya yi kira ga jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ta shiga a dama da ita, wajen samarwa kasar makoma ta fuskar siyasa.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar bayan rantsar da shi.

Ya ce zai kwatanta adalci, kuma gwamnatinsa zata kunshi kowa da kowa.

Jam'iyyar ta 'Yan Uwa Musulmi da sauran jam'iyyu masu ra'ayin Islama sun yi kira ga jama'a da su fito gobe Juma'a, domin yin zanga zangar lumana.

Shugabannin kasashen duniya suna cigaba da mayar da martani ga yanayin da ake ciki a kasar.

A baya bayan nan Tarayyar Afirka ta ce tana shirin gudanar da taro domin tattauna rikicin.

A ganin shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, kawar da zababbiyar gwamnati babban abin damuwa ne a Afirka.