Ana kama jami'in Miyetti Allah

Hukumomin tsaro a Jihar Filato dake tsakiyar Najeriya sun ce suna ci gaba da tsare sakataren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar, Malam Muhammad Nura Abdullahi.

Kawo yanzu dai hukumomi basu yi cikkaken bayani kan musabbabin kama shi ba, amma lamarin ya biyo bayan wani mummunan hari ne da wasu 'yan bindiga suka kai a Karamar Hukumar Langtang ta Kudu a makon jiya,

Hukumomin tsaro sun zargi Fulani makiyaya da kai harin bayan satar shanunsu da ake zargin wasu 'yan yankin sunyi.

A bangare guda kuma iyalan jami'in kungiyar makiyayan sun yi korafin cewa suna cikin damuwa, domin sun kasa sanin halin da yake ciki a hannun jami'an tsaron.

Bayanai dai na cewa tun a ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumomin tsaron suka kama shi tare da wasu jami'an kungiyar a kudancin jihar, bayan wani mummunan hari da wasu 'yan bindiga suka kai a wasu kauyuka na yankin.

Hari

Jami'an tsaro sun ce harin ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 28.

To sai dai kuma kusan mako guda da kama sakataren har yanzu ba bu cikakken bayani game da halin da yake ciki.

Kakakin rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar Filaton, Captain Salisu Mustapha, ya tabbatar da cewa lallai sun gayyaci sakataren domin yi masa tambayoyi; amma ya ce ba zai iya yin karin bayani akai ba.

Sai dai ya ce watakila abin na da nasaba da harin na makon jiya.

Haka kuma ya ce tuni rundunar tsaron ta kammala nata aiki ta mika shi ga rundunar 'yan sanda da kuma jami'an tsaro na farin kaya, wato SSS.

Daraktan hukumar ta SSS a jihar Filato, Mista Chris Ojobo, ya ce lallai suna ci gaba da bincike kan jami'in na Miyetti Allah.