Sojoji a Masar sun yi kiran sasantawa

Zanga-zanga a kasar Masar
Image caption Zanga-zanga a kasar Masar

Sojoji a Masar sun fitar a wata sanarwa kan kiran sasantawa ta kasa, bayan da suka tunbuke gwamnatin shugaba Morsi a ranar Laraba.

Sojojin sun ce halayyar mutanen kasar Masar na yin yafiya zai hana aikata hare-haren daukar fansa.

Sanarwar na zuwa ne bayan da kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Mohamma Morsi ta yi kiran da a fito a gudanar da zanga-zangar lumana a yau Jumma'a.

A baya dai kungiyar ta yi watsi da tayin da shugaban kasa na riko Adly Mansour yayi musu na su shiga cikin gwamnatin hadin kan kasa.

Jagoran 'yan adawar kasar Masar Mohammed El Baradei, ya shaidawa BBC cewa jami'an Sojin sun dau matakin a madadin galibin al'ummar kasar ta Masar da ba zasu taka wata rawa a dimokradiyyar kasar ba.

Mr El Baradai ya kara da cewa Idan da sojojin basu dauki wannan matakin ba, daya zabin shine yakin basasa.

Heba Morayef daraktar Kungiyar kare hakkin bil Adama ta 'Human Rights Watch' a kasar Masar, ta shaidawa BBC cewa wannan wani hali na bakin ciki ne ga dimokradiyyar kasar ta Masar.

Miss Morayef ta ce hakan ya kawo koma baya ga cigaban dimokradiyyar kasar, kana ya jefa tsaren sauya gwamnati cikin hadari.

Ta kuma ce matakin da sojin suka dauka a cikin sa'oi 24 da suka gabata, na kame da kuma rufe tashohin yada labarai, zai durkusar da al'amuran kasar.