Masar: Juyin mulki ko ba juyin mulki ba?

Zanga-zangar da ta biyo bayan hambarar da Mohammed Morsi
Image caption Zanga-zangar da ta biyo bayan hambarar da Mohammed Morsi

Shin wai yaushe ne juyin mulki ke zama ba juyin mulki ba? Ko kuma a ce akwai wani abu da za a iya kira kyakkyawan juyin mulki? Hakan zai iya nufin akwai mummunan juyin mulki ke nan?

Shin ina matsayin sojojin da suka yi wa shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, jirga in maye?

Wannan mataki nasu, menene shi?

Idan aka yi wani tunani, sai a ga cewa, wannan tambaya ba ta da wata ma'ana dama da hauni.

Domin kuwa abin da ya auku a kasar Masar wani al'amari ne wanda abin da kasashen waje za su iya yi a kai bai taka-kara-ya-karya ba.

Ciki kuwa har da kasar Amurka, wadda ake tinkaho da irin dasawar dangantaka da ke tsakaninta da sojojin kasar ta Masar.

Haka ma a shi kansa yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ke fama da rikice-rikice, babu wanda zai iya tarnake kasar Masar.

A irin tofa albarkacin bakin da ake yi game da wannan batu, wasu na cewa juyin mulki ne, wasu kuwa cewa suke yi ba juyin mulki ba ne.

Wani mai sharhi a kan al'amura a wani gidan talabijin, kwatanta al'amarin ya yi da cewa abin kyama ne.

Haka dai masu sharhi na kasashen yammacin duniya za su dade suna duba wannan batun.

Amma kuma ta wata fuskar, a iya cewa wannan tambaya tana da fa'ida.

Domin kuwa ta fito da karin haske game da martanin da manyan kasashen duniya suka mayar a kan sauyin gwamnatin kasar Masar.

Alal misali, yayin da Shugaba Barack Obama yake bayyana ta-bakin kasarsa, cewa ya yi Amurka ta yi matukar damuwa da matakin da sojojin na Masar suka dauka.

Abin da kasashen duniya dai suka fada a kan wannan batu zai zauna a zukatan jama'ar kasar ta Masar.

La'akari da hakan kuma ya bayyana taka-tsantsan da Birtaniya ta yi a nata kalaman, ko da yake sakataren harkokin wajenta, William Hague, ya yi tsokaci ne a kan siffar harshen damo da ke tattare da abin da ya auku a kasar ta Masar.

Ya bayyana al'amarin da cewa wani shiga-tsakani ne sojoji suka yi a tsarin dimokuradiyya, amma kuma ya kara da cewa wani abu ne da jama'a za su iya fahimtar dalilin aukuwarsa.

Idan aka bugi jaki aka bugi taiki, shin a iya kiran abin da ya auku a Masar kyakkyawan juyin mulki?

Muhimmin abin dubawa a nan shi ne abin da zai biyo baya.

A wani fannin dai ana ganin an yi juyin mulki ne a wani tsarin dimokuradiyya wanda alwalarsa ke tattare da lam'a.

Image caption Taswirar birnin Alkahira mai nuna wuraren da aka yi zanga-zanga da Barikin Republican Guards inda aka yi harbe-harbe

Kuma wanzuwar hakan daidai ko kuskure wani abin nazari ne ga masu sharhi a kan al'amura da masana fannin Tarihi.

Amma kuma har ila yau, wani sabon salo ne ya bayyana a kasar Masar, wanda gwamnatocin yankin da jami'an diflomasiyya na duniya baki daya ya kamata su yi la'akari da shi.

Karin bayani