Sa-in-sa kan sake binne 'ya'yan Mandela

Bangon Mandela
Image caption Bangon Mandela

Wasu manyan kasar Afrika ta Kudu biyu sun yi kira da a kawo karshen sa-in-sa din da ake kan sake binne 'ya'yan Mandelan guda uku.

Ana dai ta sa-in-sar ne tsakanin iyalan Nelson Mandela a kan batun sake binne 'ya'yan nasa.

Mataimakin shugaban kasar ta Afrika ta kudu Kgalema Motlante, ya ce yana fatan iyalan za su kawo karshen wannan rikici da suke yi ta hanyar kamala.

Shima mutumin da ya taba samun lamabar yabo ta Nebel Arch Bishop Desmond Tutu , ya roki iyalan Mandelan da kada su bata sunan Nelson Mandela da rikicin nasu.

Mutanen biyu sun yi kiran ne ya yin da aka sake binne gawarwakin 'ya'yan Mandelan a kaburburansu na ainahi a kauyen Qunu, inda tsohon shugaban Afrika ta Kudun ya taso.

Su kuwa 'yan kasar sun ci gaba da yiwa tsohon shugaban addu'oi ne a kofar asibitin da ya ke kwance.