Najeriya:'Yan bindiga sun kai hari a jihar Taraba

Harin bom a Najeriya
Image caption Harin bom a Najeriya

Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a garin Karin Lamido a daren jiya.

Wasu mazauna garin sun shaidawa BBC cewa maharan sun bankawa ofishin 'yansanda da wani banki wuta.

An kuma shafe kimanin sa'oi biyu ana ta jin karan harbe-harbe a cikin garin.

Jihohin arewacin Najeriyar dai na fama da kalubalen hare-haren da galibi ake dangantawa da 'yayan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Hare-haren dai sun haifar da asarar rayukan jama'a da dukiyoyi da dama.