An kashe 'yan makaranta da dama a Yobe

Image caption An sha kai hare-hare makamantan wadannan a yankin

Akalla mutane 30 ne aka kashe a wani hari da aka kai da sanyin safiya kan wata makarantar kwana a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an kona wasu daga cikin mutanen ne da ransu, a garin Mamudo da ke kusa da karamar hukumar Patiskum a jihar ta Yobe.

Makarantu da dama aka lalata a hare-haren da masu tayar da kayar baya suka fara kaiwa tun daga shekara ta 2010.

Jihar Yobe na daya daga cikin jihohi uku da shugaba Goodluck Jonathan ya kafawa dokar tabaci a watan Mayu.

Baya ga haka an kuma tura dubban sojoji zuwa yankin.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin, amma kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan wannan a yankin na Arewa maso Gabas.

Fiye da mutane 600 ne ake sa ran kungiyar ta kashe a shekara ta 2012, wacce ke yakar gwamnatin Najeriya da kuma hukumomin tsaron kasar.

Karin bayani