Hadarin jirgin kasa a Canada

Hadarin jirgin kasa a Canada
Image caption Hadarin jirgin kasa a Canada

'Yan sanda a kasar Canada sun ce yawan mutanen da suka mutu ya karu, bayan hadarin jirgin kasan da ya faru a garin Lac-Magnetic.

Jirgin kasan na dakon mai da ya gangaro, ya kauce daga layin dogo ya haddasa gobara a tsakiyar karamin garin na Lac-Magnetic dake lardin Quebec.

Gidaje kimanin talatin ne aka bayyana gobarar ta mamaye.

Wani jami'in kashe gobara ya shedawa kamfanin dillancin labaran faransa cewa, wutar ta barnata wata mashaya, inda mutane da dama ke dabdala a lokacin.

'Yan sanda sun ce suna dubawa su ga ko mutanen da aka bada rahotan bacewarsu 'yan yawan shakatawa ne .

Wani darektan kamfanin jirgin kasan ya ce jirgin ya gangaro ne bayan da matukinsa ya ajiye shi ya huta saboda dare ya yi.