Yobe: Za'a rufe makarantun sakandire daga gobe

Gwamnatin jihar Yobe a Najeriya ta bada umarnin rufe dukkan makarantun sakadinren dake jihar daga gobe Litinin bayan 'yan bindiga sun hallaka dalibai da malaman makarantar sakandire ta Mamudo su ashirin da biyu jiya Asabar.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Abdullahi Bego ya fitar yace, an dauki wannan mataki ne domin sake duba yadda za'a samar da cikakken tsaro ga dukkan makarantun dake jihar.

Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Geidam ya kuma ce, rufe makarantun zai baiwa hukumomin jihar da kuma rundunar tsaro ta musamman wato JTF damar fito da wasu sabbin dabaru na bullowa kalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar.

Alhaji Ibrahim Geidam ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwar wyar salula a jihar yana mai cewa, yanke hanyoyin sadarwar ya katse hanyoyin da jama'a suke amfani da su wajen taimakawa jami'an tsaro ta hanyar bada rahotanni akan masu aikata miyagun laifuka.

Jihar Yobe dai na daga cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya uku da gwamnatin tarayya ta aza dokar ta baci sakamakon karuwar hare-haren da 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram suke kaiwa.