Kamfanonin yamma zasu sa ido kan masakun tufafafi na Bangladesh

Ma'aikatan masaku a Bangladesh
Image caption Ma'aikatan masaku a Bangladesh

Akalla kamfanoni saba'in daga kasashen yammacin duniya sun kamalla shirin gudanar da binciken sa-ido a kan masana'antun dunka tufafi a kasar Bangladesh a wani yunkurin tabbatar da matakan kariya.

Kamfanonin na Turai za su bada bayanai game da masana'antun da za su bincika a cikin watanni tara masu zuwa.

Matakin ya biyo bayan rugujewar wani bene a kasar ta Bangladesh a watan Afrilu inda mutane fiye da 1,100 suka mutu.

Wakilin BBC ya ce Bangladesh ita ce kasa ta biyu mafi girma da ake fitar da kayyayakin sawa a duniya, a bara an fitar da tufafin sawa daga kasar zuwa Turai da Amurka na fiye da dala biliyon 20.