Mutane 40 sun bata a gobarar Canada

Jirgin kasan da yayi hadari a Canada
Image caption Jirgin kasan da yayi hadari a Canada

Fira Ministan Canada, Stephen Harper ya ziyarci Lardin Quebec, inda jirgin kasan dakon mai ya yi hadari ya kuma kama da wuta a ranar Asabar.

Ya ce tsakiyar birnin Lac-Megantic ya kasance tamkar fagen yaki.

Yanzu haka 'yan kwana-kwana sun kashe wutar da ta shafe sa'oi ashirin tana ci, da ta hana masu aikin ceto isa wurin da gobarar ta fi yiwa barna.

Mutane akalla biyar ne suka hallaka, yayin da arba'in suka yi batan dabo a cikin gobarar.

'Yan sanda sun ce gobabar ta yi tsananin da ta sa ba a iya gano gawawwaki da dama ma.

Will Hillary, wani ma'aikacin kafar yada labaran kasar Canada, ya ce lamarin ya kara ta'azzara cikin sa'oi 36, bayan fashewar tankar man jirgin kasar.

Ya kuma ce har yanzu akwai barazana, ta yadda ba zai yiwu a matsa kusa da tankokin ba, don har yanzu suna hucin zafi.

Fira Ministan kasar ta Canada Stephen Harper, ya ce lallai za a gudanar da bincike game da hadarin, da ya ce wani babban bala'i ne.

Mr Harper ya kuma ce wannan bala'i ya shafi duk wani mazaunin garin na Qubec, inda gobarar ta lashe gine-gine kimanin talatin, baya ga asarar rayukan da har yanzu ba za a iya hakikance adadinsu ba.