An shiga zaman dar-dar a Alkahira

Wani mutumin da ya ji rauni a Masar
Image caption Wani mutumin da ya ji rauni a Masar

Akalla mutane 42 aka harbe a kusa da barikin sojoji a birnin Alkahira, yayin da ake cigaba da samun tashin hankali a Masar, bayan hambarar da shugaba Mohammed Morsi.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Masar ta ce an harbi 'ya'yanta, yayin da suke zaman durshen a barikin dakarun dake tsaron fadar shugaban kasa.

Sai dai sojoji sun ce "Wasu 'yan ta'adda" sun yi kokarin kutsa wa cikin barikin.

Sojoji sun hambarar da shugaba Morsi wanda shi ne shugaban kasa na farko da aka zaba, bayan wata zanga-zanga a kasar.

An yi amanna cewa ana tsare da Mr. Morsi ne, a wurin shakatawar dake barikin, wanda ke gabashin gundumar birnin Nasr.

Magoya bayansa, wadanda yawancinsu 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ne, sun shiga zaman durshen tun lokacin da aka hambarar da shi.

Bayan rikicin na safiyar ranar Litinin, jam'iyyar Salafiyya Nour wacce ta goyi bayan tunbuke Mr. Morsi, ta janye daga tattaunawar zaben sabon Firai minista.

Ta kuma bayyana abin da ya faru da cewa wani "kisan kare dangi ne."

Jami'an kiwon lafiya da kungiyar ta 'yan uwa Musulmi sun ce an kashe kimanin mutane 40, yayin da wasu kimanin 300 suka jikkata a tashin hankalin.