An rufe makarantun sakandare a Yobe

Daya daga cikin daliban makarantar da aka kaiwa hari
Image caption Daya daga cikin daliban makarantar da aka kaiwa hari

A Najeriya, gwamnatin jihar Yobe da ke arewa-maso-gabashin kasar ta ba da umurnin rufe dukkan makarantun Sakandaren jihar daga ranar litinin.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Abdullahi Bego ya fitar yace, an dauki wannan mataki ne, domin sake duba yadda za'a samar da cikakken tsaro ga dukkan makarantun dake jihar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar sakandare da ke Mamudo, inda suka kashe kusan mutum talatin.

Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Geidam ya kuma ce, rufe makarantun zai baiwa hukumomin jihar da kuma rundunar tsaro ta musamman wato JTF, damar fito da wasu sabbin dabaru na bullowa kalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwar wayar salula a jihar, yana mai cewa, yanke hanyoyin sadarwar ya katse hanyoyin da jama'a suke amfani da su wajen taimakawa jami'an tsaro ta hanyar bada rahotanni kan masu aikata miyagun laifuka.

Jihar Yobe dai na daga cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya uku da gwamnatin tarayya ta sanyawa dokar ta baci, sakamakon karuwar hare-haren da 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram ke kaiwa.