Kotu ta yanke wa 'yan Boko Haram hukunci

Shugaban kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau tare da wasu 'yan kungiyar

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ta yankewa wadansu 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna lid Da'awati wal Jihad, wacce aka fi sani da suna Boko Haram, hukuncin daurin rai-da-rai.

Kotun ta yanke wa 'yan kungiyar hudu hukuncin ne bayan samunsu da laifi wajen shiryawa da kai wadansu hare-haren bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutum goma sha tara.

Hare-haren sun hada da wanda aka kai kan ofishin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) dake Suleja, Jihar Neja, a shekarar 2012.

Mai shari'a Bilkisu Aliyu, wacce ta yanke hukuncin, ta kuma bayar da umarnin daure mutum na biyar har tsawon shekaru goma a gidan kaso.

Mutum na shida da ake tuhuma kuma kotun ta wanke shi.

Wannan dai za a iya cewa shi ne karo na farko da wata kotu ta yanke hukunci mai girma, wato daurin rai-da-rai ga wadanda ake tuhuma da kai ire-iren wadannan hare-haren.

Ko da yake, a shekera ta 2011, wata kotun tarayyar ta yi wa Ali Sanda Konduga, wanda ake yiwa lakabi da Usman al-Zawahiri, daurin shekaru uku sakamakon samun shi da laifukan da suka hada da barazana da kuma kutse wa wadansu mutane.

Sai dai kungiyar ta Jama'atu Ahlis Sunna lid Da'awati wal Jihad ta ce ta dade da korarsa.

Kungiyar Boko Haram dai na fafutukar ganin an yi aiki da shari'ar Musulunci a arewacin Najeriya, kuma ta sha daukar alhakin kai wadansu hare-haren bindiga da bama-bamai a kasar, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane masu yawan gaske.