Hazem el-Beblawi ya zamo sabon Praministan Masar na riko

Hazem El Beblawi
Image caption Hazem El Beblawi

Shugaban Masar na riko, Adly Mansour, ya nada wani tsohon ministan kudin kasar, Hazem el-Beblawi, a matsayin Praministan wucin gadi.

Yayin da shi kuma Mohamed El Baradei, mai sassaucin ra'ayi, aka sanar cewa zai zama mukaddashin shugaban kasa, wanda zai kula da harkokin waje.

Jam'iyyar Islama ta Al-Nour ta goyi bayan nadin Hazem el-Beblawi.

Gwamnatin Amurka dai ta yi na'am da wannan, matakin kamar yadda aka ambaci kakakin fadar shugaban kasa Jay Carney yana cewa suna samun kwarin gwiwa daga shirye-shirye na farko da gwamnatin riko ta dauka, kuma suna baiwa kowanne bangare shawarar ya shiga cikin tattaunawar a maimakon yin fito na fito.

Game kuma da El Baradei, ta ce har yanzu tana tunani tukuna.