An kai harin bam a Beirut na Lebanon

Ta'adin da harin ya yi a Beirut
Image caption Ta'adin da harin ya yi a Beirut

Wata mota makare da bambamai ta fashe a Beirut babban birnin kasar Lebanon, a yankin da 'yan Shia na kungiyar Hezbollah suka fi rinjaye.

Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar, lamarin da ya turnuke yankin da bakin hayaki.

Fashewar ta auku ne a wata cibiyar Islama, kuma tuni 'yan kwana-kwana suka kai dauki.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon, Marwan Charbel wanda aka yiwa caa a lokacin da ya ziyarci wajen, ya yi Allah waddai da lamarin, da ya ce zai janyo zaman doya da manja tsakanin 'yan Sunni da 'yan Shi'a.

A yanzu haka dai, ana cigaba da zaman dar- dar a Lebanon din, tun bayan da mayakan Hezbollah suka shiga Syria don taimakawa shugaba Bashar al-Assad wajen murkushe 'yan tawaye.

Karin bayani