Masar ta samu tallafin kudi daga Saudiyya

Adly Mansour, shugaban riko na Masar
Image caption Adly Mansour, shugaban riko na Masar

Kasashen Larabawa biyu masu arziki sun sanarda bada taimakon makudan kudade don tallafawa kasar Masar, a wani matakin nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin kasar, tare da amincewa da tsige Shugaba Morsi.

Hadaddiyar daular Larabawa ta dauki alkawarin bada bashin dala biliyon biyu da kuma bada taimakon dala biliyon daya.

A yayinda ita kuma Saudi Arabiya ta amince da baiwa kasar tallaffin kudi na dala biliyon biyar.

Wakilin BBC ya ce cire Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi daga madafan ikon Masar, ya farantawa kasashen Larabawan biyun rai, abinda kuma ya bayyana daga irin wannan karamcin da suka yi.

Gwamnatin Masar dai na matukar bukatar tallafin kudi daga kasashen wajen don cigaban tattalin arzikinta.