Pakistan ta zargi Obama kan kisan Binladen

Image caption Pakistan ta zargi Obama kan kisan Bin Laden

Rahotannin da suke fitowa ta bayan fage na gwamnatin Pakistan na cewa, kisan da aka yi wa Osama Bin Laden shekaru biyu da suka gabata, laifin aikata kisa ne da shugaban Amurka Barack Obama ya zartar.

Amurka ta ce in da Osama Bin laden ya mika wuya da za a iya tasa keyarsa a raye.

Rahoton da gidan talabijin din Aljazeera ya samu ya kuma soki gwamnatin Pakistan da kasa gano cewa Bin Laden yana zaune a kasarta.

Rahoton ya kuma zargi manyan jami'an Pakistan da rashin sanin cewa Osama ya na zaune a kusa da makarantar horas da sojin kasar har tsahon shekaru shida daga cikin shekaru tara da ya kwashe a kasar.

Karin bayani