Tope Folarin ya lashe gasar Adabi

Image caption Dan Najeriya, Tope Florin ya lashe gasar Adabi a Birtaniya

Marubuci dan Najeriya Tope Folarin, shi ne ya lashe gasar Adabi ta Caine ta bana wadda aka yi a Birtaniya.

Littafin sa na daga cikin littattafai biyar da aka tace a karshen gasar,an tsara takaitaccen labarin Miracle a kan wani matashi da ya zo Najeriya ya kuma halarci wata Coci tare da mahaifinsa,inda wani malamin coci makaho yake warkar da wasu marasa lafiya.

Alkalan gasar sun ce littafin ya cancanci lashe gasar.

An bawa marubuci Tope Folarin Dala dubu goma sha biyar a bikin da aka yi a jami'ar Oxford ta Birtaniya.

Karin bayani