Za a kama shugaban 'yan uwa Musulmi

Shugaban kungiyar 'yan Uwa Musulmi na masar, Mohammed Badie
Image caption Shugaban kungiyar 'yan Uwa Musulmi na masar, Mohammed Badie

Ofishin gabatar da kara na Masar ya ba da umarnin kama shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi, Mohammed Badie, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Ana zargin Mr. Badie da ingiza tashin hankalin da ya faru a birnin Alkahira a ranar Litinin, inda aka kashe mutane 51.

Da dama daga cikin kusoshin kungiyar ta 'yan uwa Musulmi dai na tsare, sannan kuma an ba da sammacin kamo wasu daruruwan.

Hakan na zuwa ne yayin da sabon firai ministan kasar na rikon kwarya, Hazem Al-Beblawi ke shirin kafa majalisar ministoci.