Beblawi: Kalubalen zaben ministoci

Sabon Firai ministan Masar, Hazem al-Beblawi
Image caption Al-Beblawi shi ne tsohon ministan kudin Masar

Sabon Firai ministan Masar, Hazem al-Beblawi ya fara aikin hada majalisar ministoci, mako daya bayan soji sun hambarar da shugaba Mohammed Morsi.

Kuma ana sa ran Mr. Beblawi zai yi tayin bada wasu mukamai ga kungiyar 'yan uwa musulmi, ko da yake ta ki ba da goyon baya ga abin da ta kira juyin mulki.

Jam'iyya mai ra'ayin sassauci ta ce ba a shawarce ta ba wajen daukar dokar, saboda haka tana son ayi wasu sauye-sauye.

Amurka dai ta ce "Tana samun cigaban kwarin gwiwa" game da yunkurin da ake na yin garonbawul.

Shugaban rikon kwarya Adly Mansour ne ya sanar da sabon jadawalin zabe a ranar Litinin, sa'oi bayan kisan mutane 51 mafi yawansu mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi.