Talauci ya jawo raguwar haihuwa a Turai

Image caption Mace mai juna biyu

Wani sabon bincike da cibiyar Max Planck ta Jamus ta gudanar ya nuna cewar an samu raguwar haihuwar jarirai a nahiyar Turai, tun bayan da aka fara fuskantar koma bayan tattalin arziki.

Wata cibiyar ta ce haihuwar ta ragu, dai dai da yadda ake samun karuwar rashin aikin yi.

Binciken ya gano cewa lamarin ya fi kamari a kudancin Turai musamman a tsakanin matasa wadanda suka yanke shawarar kin haihuwa saboda rashin aiki.

A kasar Spain an samu raguwa wajen haihuwa da kashi takwas cikin dari daga shekara ta 2008 zuwa 2011.

Amma kuma a kasashen Jamus da Austria da kuma Switzerland, inda rashin aikin yi bai yi kamari ba sosai, an samu daidaito wajen hayayyafar da mata ke yi.

Karin bayani