'Yan uwa Musulmi sun bijirewa mukamai

Image caption Jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi ta bijirewa mukamai

Jamiyyar 'Yan uwa musulmi ta Masar ta shaidawa BBC za ta bijirewa duk wani mikami na gwamnati, a sabuwar gwamnatin Firaminista Hazem el- Beblawi.

Batun sasantawa shi ne abin da Mr el Beblawi ya sa a gaba bayan da aka nada shi.

Jamiyar 'Yan uwa musulmi ta ce ba za ta iya amincewa da komai ba, idan ba dawo da hambararren shugaban Mohammed Morsi ka mukaminsa ba.

Gwamnatin rikon kwaryar dai na fuskantar suka daga Jamiyyar hadaka mai sassaucin ra'ayi.

Karin bayani